Taimakon makarantu da littattafai | Sauyi a Afirka | DW | 22.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Sauyi a Afirka

Taimakon makarantu da littattafai

Wani mai kishin kasa a Nigeria ya kaddamar da wani mataki a makarantu ga dalibai ta hanyar raba littattafai a kan kiyaye dokokin kasa, dan chanza fasalin yadda ‘yan Nigeria ke da gurguwar fahimtar ayyukan ‘yan sanda.

A karan farko wani mai kishin kasa da ke aikin sa-kai na wayar da a kan mutane, ya kaddamar da wani gangami a makarantun kasar mai taken "Dan Sanda Abokin Kowa " saboda wayar da kan dalibai gami da karfafa dangantaka tsakanin ‘yan sanda da al'umma kasa ta hanyar rarrabawa dalibai littattafai da ke kunshe dokokin kasa, domin rage aikata laifuffuka, da zumar gane duk ayyukan jami'an tsaro dalla-dalla dan tabbatar da ganin cewa rage kallan tsoran da ake yi wa ‘yan sanda wanda zai takama masu samun bayanai.

Comrade Abdullahi Ladan shi ne dai matashin da ya kaddamar da shirin fadakarwa tsakanin ‘yan sanda da al'umma inda yake bayyana cewa yawancin matasan Nigeria ba su da wata masaniya a kan dokokin kasar ballantana ma kokarin sanin ‘yancinsu, a saboda haka muna ganin cewa lallai dai kam akwai gagarumin aikin da ya wajaba.

Littattafai kala 2 ne dai marubucin ya rubuta, daya da harsken Turanci kana daya da harshen Hausa, kuma kowane na dauke da wasu hutunan da ke bayyana wasu laifuffuka, da gargadin matasa kan hanyoyin ragakafin kauce musu.