1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon Kungiyar EU ga al´umar Falasdinawa

June 23, 2006
https://p.dw.com/p/Busu

Hukumar zartaswar KTT ta ce zata fara turawa Falasdinawa taimakon na Euro miliyan 105, ba tare da kudaden sun bi ta hannun gwamnatin dake karkashin jagorancin kungiyar Hamas ba. Hukumar ta EU ta ce a farkon watan yuli za´a tura wannan tallafi. A ranar lahadi da ta gabata bangarorin hudu dake shawarwarin samar da zaman lafiyar yankin GTT wato kungiyar EU, MDD, Amirka da kuma Rasha suka albarkaci sabon shirin talafawa Falasdinawa dake fama da matsalolin karancin kudi. To amma kudaden ba zasu shiga hannun Hamas ba wadda ta ki yin watsi da tashe tashen hankula kana kuma taki amincewa da wanzuwar Isra´ila. A jiya kuwa an gana tsakanin FM isra´ila Ehud Olmert da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a gun wani taro a Jordan kan halin da ake ciki a GTT. FM Olmert ya ce sun yarda su sake ganawa a cikin mako mai zuwa. Shi ma Abbas ya ce ganawar ta su ta yi armashi.