Taimakon Jamus ga Afganistan | Siyasa | DW | 19.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taimakon Jamus ga Afganistan

A wannan Talatar ake gudanar da babban taron duniya kan tallafawa ƙasar Afganistan a birnin Kabul

default

An tsaurara matakan tsaro sabili da taron na birnin Kabul

Daga cikin ƙasashen dake taimakawa wannan ƙasa dai har da tarayyar Jamus wadda tun a shekarar 2002 take tafiyar da aikin sake gina Afganistan. Sojoji da 'yan sanda da kuma ma'aikatan taimakon raya ƙasa daga Jamus suna aiki kafaɗa da kafaɗa domin tallafawa ayyukan gamaiyar ƙasa da ƙasa a Afganistan.

Ƙungiyoyin agajin daga Jamus, suna gina makarantu, suna aiki a asibitoci musamman wajen yaƙi da mace-macen yara da mata a wurin haihuwa. Suna kuma ba da ƙananan basussuka ga manoma da makiyaya.

Krankenhaus in Kunduz

Asibiti a yankin Kundus

To sai dai duk da jerin ayyuka masu yawan gaske da ƙungiyoyin agajin na Jamus, manyan da ƙananan ke yi a Afganistan, amma abin baƙin ciki shi ne ba a faye mayar da hankali kansu a rahotanni game da rigingimun ƙasar ba. Alal misali ƙungiyar likitoci ta "Doctors Without Borders" wadda ta shafe shekaru 24 tana ba da gudunmawa a Afganistan, yanzu haka dai ya zame mata tilas ta ɗauki matakai biyo bayan harbe ma'aikatanta guda biyar har lahira a wannan shekara kaɗai, kamar yadda shugabanta Tankred Stöbe ya tabbatar.

"Mun janye saboda kaɗuwar da muka yi. To amma saboda taɓarɓarewar harkar kiwon lafiya, a dole mun tattauna da dukkan ɓangarorin dake faɗa da juna, kafin mu yanke shawarar komawa."

A sabili da barazanar da ma'aikatan agaji ke fuskanta ya sa a tilas wasu ƙungiyoyin taimako sun rage yawan ma'aikatansu na ƙetare musamman ma 'yan yamma. Babban ciƙas ɗin dai ba daga yaƙin ba ne kaɗai, a'a har ma da rashin amincewa da taimakon daga ɓangaren jama'a da kuma shugabannin hukumomin yankunan ƙasar ta Afganistan. To sai dai hakan bai sa ƙungiyoyin sun yi ƙasa a guiwa ba. Alal misali ƙungiyar likitoci ta ƙasa da ƙasa tana tafiyar da aiki a wani asibiti ɗaya daga cikin asibitoci biyu dake lardin Helmand mai hatsarin gaske. Saboda yanayi na yaƙi yasa marasa lafiya na tsoron zuwa neman magani.

Herat Zentrumspark

Wurin shaƙatawa a tsakiyar birnin Herat, dake nuni da nasarar aikin sake gina Afganistan

To sai dai har yanzu akwai wurare da dama a ƙasar ta Afganistan inda ƙungiyoyin agajin ke tafiyar da aikinsu ba da tsangwama ba. Alal misali ƙungiyar agaji ta "Shelter now" ta gina asibitin haƙori a yankin Herat inda ake horas da likitocin haƙori bisa matsayin ilimi na Jamus da Turai. Udo Stolte na reshen "Shelter now" a Jamus ya san wuraren da ba za a iya zuwa ba.

"Ba za mu iya shiga yankunan Pashtun ba. A can ƙungiyoyi kaɗan ne ke aiki, hakan kuwa abin baƙin ciki ne, domin ɗaukacin al'umar 'yan Pashtun ne. Wannan wani hali ne mawuyacin gaske."

A wasu wurare sai da jiragen sama ake iya kai ɗaukin da ake buƙata. Yayin da 'yan agajin kan samu kansu a tsakiyar mayaƙa. A saboda haka wasunsu ke canza wuraren gudanar da aikinsu, kamar wasu Jamusawa da yanzu suka koma arewacin ƙasar inda aka girke dakarun Jamus. A duk inda ƙungiyoyin agajin suke a Afganistan dai, suna cin karo da matsalolin cin hanci daga jami'an gwamnati dake neman na goro kafin su ba da izinin yin aiki.

Mawallafa: Wolfgang Dick/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu