Taimakon da Musulmi a nan Jamus ke bayarwa dangane da Tsunami | Siyasa | DW | 10.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taimakon da Musulmi a nan Jamus ke bayarwa dangane da Tsunami

A yayinda kasashen Larabawa suka fuskanci suka sakamakon daridari da suka yi wajen ba da taimako ga mutanen da bala'in tsunami ya rutsa da su, Musulmi a nan kasar sun tashi gadan-gadan ne wajen ba da taimakon da ya cancanta

A duk lokacin da jama’a suka hallara a masallatai domin i da salla, limamai kan yi amfani da wannan dama domin kiran ba da kudade da sauran taimako na sadaka dangane da mutanen da masifar mahaukaciyar igiyar ruwa ta tsunami ta rutsa da su. Irin wannan kira dai abu ne da akas saba gani yake kuma daya daga cikin shikashikan musulunci na fid da zakka domin taimakon gajiyayyu marasa galihu. Musulmi a nan kasar gaba daya suka rika amsa wannan kira domin ba da taimako, kowane gwargwadon ikonsa. Wasu daga cikin Musulmin, kamar yadda bayani ya nunar, a baya ga taimakon da suka gabatar a masallatai, kazalika sun amsa kiran kafofin taimako na kasa da kasa domin ba da gudummawa ta bankuna. Da yawa daga musulmin sun bayyana bakin ciki da takaicin cewar kasashen Larabawa, wadanda Allah Yayi musu arzikin mai sun ki su ba da taimako daidai yadda ya kamata, har ya kai ga fuskantar suka daga MDD. A lokacin da yake bayani game da haka, wani dalini daga kasar Libiya cewa yayi:

Wannan a hakika abin kunya ne. Domin, kamar yadda na gani da idanu na ta akwatin telebijin, ainifin wadanda suka fi zautuwa daga wannan bala’i musulmi ne ‚yan kasar Indonesiya. Ta la’akari da haka, da kamata yayi a ce kasashen Larabawa da na Musulmi baki daya sune akan gaba wajen gabatar da taimako, wanda wani bangare ne da addinin musulunci.

A daura da haka dai Musulmi a nan kasar sun shiga gadan-gadan aka rika damawa da su wajen tara kudaden gudummawar. A halin yanzu haka akwai Musulmi masu tarin yawa da suka tsayar da shawarar yin amfani da kudadensu na layya a ranar 20 ga watan nan na janairu, domin taimaka wa mutanen da bala'an ya rutsa da su A Asiya. Kungiyar Muslmi Turkawa ta gabatar da wani matakin gangami na kiran ba da taimako a masallatanta kimanin 870 dake sassa dabam-dabam na Jamus. A lokacin da aka nemi jin ta bakinsa, Imam Fehmi Güler dake nan birnin Bonn ya bayyana gamsuwarsa da azamar da Musulmin ke nunarwa wajen ba da kudaden taimako, inda yake cewar:

A musulunce babu wani banbanci, walau na addini ko na launin fata dangane da mabukata dake neman taimako. Nan ba da dadewa ba zamu yi bikin sallar layya, inda ya wajaba mu hada da makobtanmu da ba musulmi ba wajen rabon nama. Domin su ma makobtanmu ‚yan-Adam ne da Alla Ya halitta ya kuma nufe su da bin wani addin dabam. Kawo yanzun dai kungiyar Musulmin ta Turkawa ta tara dubban daruruwan takardun kudi na Euro domin taimako ga Bayin Allahn da bala’i ya rutsa dasu a kudancin Asiya. In dai ba a manta ba ita ma Turkiyya sai da tayi asarar mutane sama da dubu 15 sakamakon wata girgizar kasar da ta rutsa da ita a cikin watan agustan shekara ta 1999.