Taimakon Bankin Standard ga manoma a Afirka. | Labarai | DW | 04.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taimakon Bankin Standard ga manoma a Afirka.

An fara wani taron masu ruwa da tsaki a harkar noma a ƙasar Ghana.

default

Gonar koko a Ghana.

A jiya Juma'a ne Bankin Standard a Afirka ya yi shelar ware kuɗi dalar Amirka miliyan 100 domin tallafa wa ƙananan manoma dubu 750 a ƙasashen Ghana da Mozambik da Tanzaniya da kuma Uganda da nufin bunƙasa kayayyakin noman da suke samarwa. Shugaban Bankin, Clive Tasker ya shaida wa wani taron masu ruwa da tsaki a harkar noma a nahiyar Afirka, wanda birnin Accra na ƙasar Ghana ke ƙarbar baƙuncinsa cewar, akwai buƙatar taimaka wa manoma masu zaman kansu, domin bin sahun rawar da hukumomi ke takawa da nufin ƙara yawan albarkatun noman da nahiyar Afirka ke samarwa. Shugaban Bankin na Standard ya ƙara da cewar, rancen da bankin zai bayar tare da ƙawancen wata ƙungiyar bunkasa sha'anin noma a nahiyar Afirka wadda aka fi sani da "Alliance for a Green Revolution in Africa", zai fi ba da fifiko ne ga noman koko da kuma kanju.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas