1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon agaji ga nahiyar Afirka

Mohammad Nasiru AwalNovember 7, 2003
https://p.dw.com/p/Bvnj

A nahiyar Afirka kimanin kashi 80 cikin 100 na al´ummomin wannan nahiyar na rayuwa da kasa da Euro biyu a rana, sannan kashi biyu cikin uku ba su da tsabtattacen ruwan sha yayin da nahiyar ta kasance kan gaba wajen fama da matsalolin cututtuka kamar zazzabin cizon sauro da kuma AIDS ko SIDA. Don ganin an dauki sahihan matakan inganta halin rayuwar al´ummomin wannan nahiya, a karon farko cikin tarihin Jamus, wasu kungiyoyin ba da agaji 26 na Jamus sun fara wani gagarumin shiri, inda suka yi kira ga jama´ar wannan kasa da su tashi tsaye wajen taimakawa Afirka. Kungiyoyin da suka hada da Caritas da Malteser da kungiyar taimakawa kananan yara da dai sauransu, sun nada shahararren mawaki Bajamushe, Herbert Grönemeyer, wanda bai dade ba da dawowa daga wata ziyarar aiki ta mako daya a kasashen Kongo da Rwanda, a matsayin jakada na wannan gagarumin aiki. Yayin wannan rangadi Grönemeyer ya ziyarci asibitocin nakasassu da wuraren da ake koya musu sana´o´i da kuma kera kekunan guragu. Grönemeyer ya bayyana cewa wannan ziyara ta karfafa masa guiwa musamman ganin yadda nakasassu ke mayar da himma wajen koyan sana´o´i don inganta halin rayuwarsu, duk da matsaloli iri dabam dabam da suke fuskanta. A dai halin da ake ciki daukacin Jamusawa ba su da wata masaniya game da matsalolin talauci, yake-yaken basasa da cututtuka kamar AIDS da Malaria da suka addabi nahiyar Afirka. Saboda haka kungiyoyin ba da agaji ke fatan cewa wannan shiri da suka sa a gaba zai jawo hankalin jama´ar wannan kasa su san irin mawuyacin hali da ´yan Afirka ke ciki don su nuna zumunci ga al´ummomin wannan nahiya ta yadda watakila su ma halin rayuwarsu zai inganta. Yayin da suke yin kira na hadin guiwa dukkan kungiyoyin da suka shiga cikin wannan shiri sun jawo hankalin jama´a cewa a nahiyar Afirka akwai mutane da ke kokarin taimakawa kansu da kansu, to amma duk da haka suna bukatar taimako daga ketare don samun wani ci-gaba mai dorewa. Bugu da kari ayyukan da kungiyoyin ba da agaji ke gudanarwa a Afirka na bukatar taimako, muddin ana son a cimma manufar da aka sa a gaba, inji Susanne Anger mai magana da yawun kungiyoyin agaji. Yanzu haka dai kungiyoyin sun fara wani shiri da nufin wayar da kan jama´a a fadin tarayyar Jamus game da wannan gagarumin aiki da suka sanya a gaba don taimakawa nahiyar Afirka.