Taimako daga KTT domin aikin kiyaye zaman lafiyar Darfur | Siyasa | DW | 05.07.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taimako daga KTT domin aikin kiyaye zaman lafiyar Darfur

Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar NATO zasu ba da taimako domin tsugunar da sojan kiyaye zaman lafiya na kasashen Afurka a lardin Darfur

Kungiyar Tarayyar turai ta yi wa ta Tarayyar Afurka tayin taimakon kwararru da jigilar dakarun soja da motoci masu sulke da da sauran kayan aiki na soja da ake bukata domin tafiyar da matakin na kiyaye zaman lafiya a lardin Darfur na kasar Sudan. Gaba daya Kungiyar Tarayyar Turai ta tanadi jumullar kudi na Euro miliyan 170 domin tallafa wa matakin, inda za a ware Euro miliyan 122 a matsayin tallafi ga basussukan dake kann Kungiyar Tarayyar Afurka yanzu haka. Kungiyar Tarayyar Turai na sa ran ganin an gabatar da matakin nan take, bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi a zamanin baya, ta yadda za a cimma adadin sojoji dubu takwas da aka kuduri niyyar tsugunarwa a Darfur nan da watan oktoba mai zuwa. Sai dai kuma a zauren taron kolin Kungiyar Tarayyar afurka da ake gudanarwa a Libiya, kantoman kungiyar akan al’amuran tsaro da zaman lafiya said Djinnit yayi kiran ba da karin taimako. A baya ga jami’an soja masu sa ido su 16 kasashen Turai ba zasu tura sojojinsu zuwa Darfur a matakin na kiyaye zaman lafiya ba, saboda adawa daga gwamnatin Sudan da kuma ita kanta Kungiyar Tarayyar Afurka. A wannan mataki ba a bukatar ganin jar fata. Ana fata kafin nan da watan oktoba mai zuwa jiragen saman jigilar dakarun soja na Kungiyar Tsaro ta NATO da Kungiyar Tarayyar Turai zasu kwashe sojojin dubu bakwai zuwa kasar Sudan, inda za a karkasasu runduna-runduna da kowace ke da sojoji dubu karkashin inuwarta. Sojojin sun hada da na Nijeriya da Ruwanda da Afurka ta Kudu da kuma Senegal. A baya ga haka an kara yawan ‚yan sandan da ake da niyyar tsugunarwa a lardin na Darfur daga dakaru 800 zuwa dakaru 1600. Ita dai KTA, babban fatanta shi ne ta tsugunar da sojoji dubu 12 a lardin Darfur nan da shekara mai zuwa, domin dakatar da matakai na tashe-tashen hankula da fatattakar mutane daga yankunansu na asali tare da share hanyar komawar ‚yan gudun hijira zuwa gidajensu. To sai dai kuma kungiyoyin taimakon jinkai sun nuna cewar da wuya a iya daukar wani matakin tsaron da zai zama gama-gari a lardin na Darfur mai fadin murabba’in kilomita dubu 500. Jami’an diplomasiyyar kasashen KTT sun yi korafi a game da tafiyar hawaniyar da ake samu daga bangaren KTA, wacce ke fama da gibi a matakan kiyaye zaman lafiya da rashin isassun kayan aiki a kasar Sudan. A karkashin wani mataki na gaggawa KTT zata ba wa sojojin kiyaye zaman lafiyar na kasashen Afurka horo a cikin watan nan na yuli da kuma watan agusta mai kamawa. Alkaluma masu nasaba da MDD sun kiyasce cewar kimanin mutane miliyan biyu da dubu 400 aka fatattakesu daga gidajensu, sannan wasu dubu 300 kuma suka yi asarar rayukansu tun bayan ballewar rikicin lardin Darfur misalin shekaru uku da suka wuce. Kungiyoyin taimakon jinkai sun gabatar da gargadi a game da fuskantar matsalar yunwa da ka rutsa da wannan lardin. Kuma akwai bukatar taimakon barguna da kwanuka da sauran kayayyaki na girki tun kafin damina ta kankama a Darfur, inda aka ce kimanin mutane miliyan uku ne suka dogara kacokam akan taimakon abinci a yankin yanzu haka.