1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

040110 Dialog Migranten Lehrer

January 27, 2010

A nan Jamus malaman makarantu ƙalilan ne ke da asali da ƙasashen ƙetare, to amma a daura da haka a manyan biranen ƙasar kimanin kashi 50 cikin 100 na ´yan makaranta na da asali da ƙasashen ƙetare.

https://p.dw.com/p/LhiL
Yaran baƙi a wata makarantar koyan sana´aHoto: picture-alliance/ dpa

Don magance wannan matsala ta ƙarancin malamai baƙi, an fara wani shirin taimakawa masu sha´awar sana´ar koyarwa dake da asali da ƙasashen ƙetare.

Bisa wani ƙiyasin da aka yi, kimanin kashi biyu cikin 100 kaɗai na malaman makarantu a nan Jamus na da asali da ƙasashen ƙetare. Wannan adadin ya yi kaɗan ƙwarai da gaske idan aka kwatanta da yawan ´yan makaranta masu wannan asali. A halin da ake ciki fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙananan yara a manyan biranen wannan ƙasar, na da tushen al´adu guda biyu. Akan haka gidauniyar Hertie ta fara wani shirin tallafawa Jamusawa masu tushe da ƙetare dake sha´awar karantarwa a makarantu. Waɗanda wannan gidauniyar take tallafawa daga jihohi huɗu na wannan ƙasa su haɗa da ɗalibai da malamai dake neman sanin makamar aiki da kuma masu karatun neman ilimi mai zurfi a jami´a.

Wannan dai halin da ake ciki ne a wani ɗakin taron ƙarawa juna sani dake birnin Hamburg, inda ɗalibai 10 dake samun tallafin gidauniyar ta Hertie ke tattaunawa. A gaban su an baza katuna kimanin 50 masu ɗauke da bayanai daban daban. Kowane daga cikinsu ya kan ɗauki guda ɗaya ya gabatar a gaban takwarorinsa.

“Suna na Behnam Saliminia. Wataƙila za ku yi mamaki, wannan suna dai na mutanen Persha ne, kuma Behnam ake kira na amma ba Bechnam ba kamar yadda wasu suke yi.”

Kusan dukkansu sun san sunan juna da kuma yadda ake faɗarsa. Daga cikin su akwai waɗanda ko dai su ne suka zo wannan ƙasa ko kuma iyayensu ne suka yi ƙaura zuwa Jamus daga ƙasashe kamar Peru, Ghana, Afghanistan, Poland ko kuma Kuretiya. Tun suna yara ƙananan sun shafa faɗi tashi a rayuwarsu a nan Jamus, musamman dangane da wariya da ake nuna musu, ko rashin iya Jamusanci ko rashin yarda da kai cewa za ka iya yiwa kanka wani abin kirki.

To sai dai duk da haka sun ci jarrabawar shiga jami´a da shahada mai kyau, kuma yanzu haka suna karatu a jami´o´in wannan ƙasa a fannin koyan sana´ar karantarwa.

Dukkansu suna ɗaukar shirin ba da tallafin na gidauniyar Hertie da muhimmancin gaske. A kowane wata ana taimakawa waɗannan matasan ´yan shekarun haihuwa tsakanin 20 zuwa 30, da kuɗi tsakanin euro 600 zuwa 2000. Hakan na taimakawa su mayar da hankali kacokan kan karatun jami´a. Kasancewar ɗaukacinsu iyayensu ba masu kuɗi ba ne, wannan tallafin na zama wata ni´ima a garesu. Taron ƙarawa juna sanin da suke halarta wani ƙarin ilimi na kyautata zamantakewa da ƙara musu ƙarfin guiwa. Hakazalika yana ba su damar sanin sabbin fasahohi da dubarun aiki.

Shugabar taron Anna von Klencke ta yi ƙarin bayani kan taron na ƙarawa juna sani tana mai cewa.

“Wannan taron ƙarawa juna sani kan abubuwan da aka sa gaba yana taimakawa mahalarta sun san alƙiblar da za su dosa na neman ƙarin ilimi. Abubuwan da ake mayar da hankali kai a karatun ƙarin ilimi yana da muhimmanci ga sana´ar da mahalarta taron ke sha´awar yi nan gaba. Abin nufi shi ne dukkan abubuwan da suka ƙuduri aniyar yi a wannan wuri, za su ga fa´idarsa a makarantun da za su koyar.”

Tun yanzu mahalarta wannan kwas sun fara cin gajiyar wannan shirin ba da tallafin. Baya ga karatu da suke yi a jami´o´i, suna kuma taka rawa a aikin ba da ilimi a duk lokacin da suka samu sarari. Alal misali wata da ake kira Gloria Boateng haifaffiyar ƙasar Ghana, tun tana da shekaru 10 ta zo Jamus inda ta samu reno daga iyayen riƙo. Yanzu haka ta na karatun neman digirgir.

“A lokaci guda ina karatun neman digirgir a jami´a sannan a lokaci ɗaya kuma ina matsayin malama ga waɗanda ake tallafa musu da kuɗin karatu. Wato kenan ina matsayin tsaka-tsaki a tsakanin gidauniyar dake ba da wannan tallafi da kuma masu karɓar tallafin. A kullum muna musayar ra´ayoyi akan aikinmu da yadda za mu inganta shi da irin ci-gaban da ake samu tsakanin ɗalibai da masu ba da tallafin kuɗin karatun wato sukolashif. Aiki na dai shi ne kulawa da kuma ba da shawara.”

Tun a jami´a Gloria Boateng da Behman Saliminia sun juna wato gabanin wannan shiri na sukolaship. Sun kafa wata ƙungiya mai da sukawa suna Schlaufox, wadda membobinta ke taimkawa yara da matasa dake kan hanyar kammala makarantun sakandare.

Duk ranar da bai je jami´a ba Behman yana amfani da lokacinsa wajen kula da ´yan makaranta ƙarƙashin ƙungiyar Schlaufox. Ita kuwa Gloria aikinta shi ne tsara aikin ƙungiyar. To sai dai ba kowa ne ya san muhimancin wannan taimakon da suke bayarwa ba, domin sau da yawa yaran su kan ƙi halartar wuraren ba da darasin. A saboda haka mutanen biyu suka fara tuntuɓar iyayen yara domin sanin dalilin da kan sa yaran ba sa son zuwa aji.

Dole sai an haɗa hannu da hannaye tsakanin masu kula da yara da ´yan makaranta da malamai da kuma iyaye kafin yaran su ci jarrabawar kammala makaranta. Ra´ayoyin masana sun ɗaya cewa ana buƙatar ƙarin malaman makarantu masu asali da ƙasashen ƙetare.

Yanzu haka dai Gloria Boateng tana rubuta kundin neman digirgir a fannin koyarwa a makarantun ɗalibai da suka fito daga ƙasashe daban daban masu bin al´adu da addinai daban daban. 

“Wataƙila malamai ko mutane masu tushe da ƙasashen ƙetare sun fi amincewa da waɗannan yara. Wannan shi ne. Wani abin kuma shi ne suna zaman abin koyi ga yaran. Domin a tunaninsu wata rana za su iya taka rawa irin ta masu taimakawa a matsayinsu na malamai Jamus. Ta haka za su iya taimakawa yara a wasu fannoni daban.”

Shi kuwa Behman fata yayi cewa nan ba da daɗewa ba zai nuna ƙwarewarsa a matsayin malamin makaranta a azuzuwa. Sannan sai ya ƙara da cewa.

“Yanzu shekara ta uku kenan a jami´a wato ina semester ta shida, kuma a semester ta gaba zan fara aikin koyarwa na sanin makamar aiki a makaranta na tsawon makonni shida. A nan ina fata zan samu sukunin faɗaɗa ilimi na da ´yar ƙwarewar da nake da ita kawo yanzu. Ina matuƙar farin ciki da wannan damar da na samu. A kullum ina farin cikin aiki da matasa. Na yi imani zan ji daɗin wannan aiki.”

Mawallafa: Ute Hempelmann/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Ahmed