Tahirin marigayi Ado Gwadabe
July 13, 2015Talla
Marigayi Ado Gwadabe tsohon shugaban Sashen Hausa na DW an haife shi a shekarar 1939 a birnin Kano da ke Najeriya, kuma ya bar duniya ranar 21 ga watan Yuni na 2015, yana da shekaru 76 a duniya.
Kuma ya yi karatu a birnin Kano kafin zarcewa zuwa birnin Moscow na kasar Rasha, inda ya kara karatu, daga bisani ya fara aiki da tashar DW. Kafin ya tafiya kasashen ketere marigayi ya yi aikin koyarwa a wasu kananan makarantu da ke birnin Kano.
Marigayin ya fara aiki da DW a farkon shekatru 1970, sannan ya zama shugaban Sashen Hausa a shekarar 1993 inda ya yi shugabancin zuwa 2004.
Ya bar mata da yara hudu.