Tagwayyen hare hare a Mogadisiyo | Labarai | DW | 09.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tagwayyen hare hare a Mogadisiyo

' Yan ƙungiyar Alshabab sun ɗoki alhakin kai hare haren da suka kashe mutane da dama a filin sukar jiragen sama na birnin Mogadisiyo

default

Rahotanin daga birnin Mogadisiyo na ƙasar Somaliya na cewa wasu tagwayyen hare hare guda biyu da aka kai a filin saukar jiragen sama birnin, sun yi sanadiyar mutuwar muatane takwas galibi sojojin rundunar kiyaye tsaro ta ƙasa da ƙasa ta Amisom.

Shaidu sun ce ɗaya daga cikin maharan ya tayar da bam ne a cikin motarsa a kusa da filin saukar jiragen saman ,yayin da ɗaya dan ƙunar baƙin waken ya darkaki sojojin dake gadin filin jirgin.Masu aiko da rahotannin dai sun ce a yan ƙwanakin baya baya nan dai yan ƙungiyar na Al shabab sun daɗa kai hare hare akan mayan gine gine gwamntin,

wanda ,ko a makon jiya sai da wasu sojojin guda fuɗu na kungiyar Amisom suka mutu a cikin wasu hare haren da yan tawayyen suka kai

Mawallafi: Abdurahamane Hassane

Edita : Ahmad Tijani Lawal