1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tagwayen hare-haren ta'addanci a Najeriya

June 21, 2011

ƙungiyar Boko Haram ta salwantar da rayukan mutane bakwai lokacin da ta kai wasu jerin hare hare ta'addanci a wani gari da ke da tazarar kilometa 130 da birnin Katsina na arewacin tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/11fv1
Wata mota bayan harin barin 'yan sanda a Port harcourtHoto: AP

A Najeriya, Ƙungiyar da ake yi wa laƙabi da Boko Haram ta sake ƙaddamar da wasu tagwayen hare-hare akan wani caji ofis ɗin 'yan sanda da kuma wani banki a ƙankƙara da ke jihar katsina inda mutane bakwai suka raya rayukansu. Waɗannan suka shaidar da tashin bama-baman suka ce daga cikin waɗanda suka riga mu gidan gaskiya har da 'yan sanda guda biyar. Wannan harin ya zo ne kwanaki biyar bayan na haedkwatar ɗin 'yan sandan Najeriya a Abuja wanda inda aka samu salwantar rayukan mutane biyu.

Kanfanin dillacin labaran Faransa wato AFP ya nunar da cewar wasu mutane da ake kyautata zaton cewar 'yan Boko Haram, ƙungiyar da ke alaƙanta kanta da taliban ɗin Afghanistan ne suka tayar da bama bamai a ƙanƙara, garin da ke da tazarar kilometa 130 da birnin katsina. wasu jerin hare-haren sama da goma ne ƙungiyar ta ɗauki alhakin ƙaddamar da su a watannin baya-bayan nan da nufin ɗaukan fansa bayan kashe shugabanta da hukuimomin najeriya suka yi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu