Tagwayen hare-hare a Rasha | Labarai | DW | 03.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tagwayen hare-hare a Rasha

Rahotannin da ke fitowa daga birnin Moscow na kasar Rasha, na cewa akalla mutane 10 ne suka mutu a wasu tagwayen hare hare a tashar jiragen kasa da ke birnin St. Petersburg.

Tagwayen hare-hare a birnin St. Petersburg na Rasha

Tagwayen hare-hare a birnin St. Petersburg na Rasha

Kamar dai yadda jami'an agaji suka tabbatar hare-haren sun afku ne a tashar jiragen kasa ta karkashin kasa da ke birnin St. Petersburg. Daya daga cikin hare-haren a cewar jami'an agajin, nakiya ce da ke dauke da muggan karafa. Rahotanni sun nunar da cewa kawo yanzu a kalla mutane 20 ne suka jikkata sakamakon harin, yayin da aka rufe baki dayan tashoshin jiragen kasa na karkashin kasa a birnin na St. Petersburg.