1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tagwayen bama-bamai sun fashe a Kamaru

Pinado Abdu WabaSeptember 3, 2015

Harin ya afku ne a Kerawa da ke yankin Arewa mai nisa inda Kamaru ta dade tana kokarin dakile hare-haren Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1GQn1
Kamerun/ Soldaten/ Boko Haram
Hoto: picture-alliance/dpa

Wasu tagwayen bama-bamai sun fashe a wani kauye da ke yankin arwacin Kamaru, rahotanni sun ce wannan kauyen ne ma kungiyar Boko Haram ta taba kai wa hari a watan Fabrairun da ya gabata, bisa bayanan da sojoji da jami'an kasar suka baiwa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Rahotanni sun ce wurare biyu aka kai harin, na farko a kasuwar Kerawa kafin daga bisani wani bam din ya sake fashewa a wani sansanin horaswar soji.

Wani wanda bai bayyana sunan shi ba ya ce akwai rahotannin da ke cewa mata ne suka kai wannan harin sai dai ba a riga an tantance gaskiyar wannan hasashen ba. Duk da cewa Boko Haram ba ta dauki alhakin wannan hari ba, ana zargin irin salonta ne domin ko a watan Yuli ta kai hari a Maroua wanda shi ma ke yankin na Arewa mai nisa, inda nan ma mutane da dama suka hadu da ajalinsu.