Tagwayen bama-bamai sun fashe a Algiers
December 11, 2007Talla
Wasu tagwayen bama-bamai sun fashe a cikin wata mota ƙirar Bus a birnin Algiers na ƙasar Algeria. Mutane 57 ne su ka rasa rayukansu, wasu kuma da dama su ka jikkata. Bom na farko a cewar rahotanni ya fashe ne a kusa da kotin ƙolin ƙasar. Bom na biyu kuma ya ta shi ne a yankin da gidajen Jami´an diplomasiyya su ke. Babu dai wani mutum ko ƙungiyya da ta yi ikirarin hannu a cikin harin, to amma bincike kan hakan na ci gaba da gudana.