Tada jijiyar wuya tsakanin kasashen EU | Labarai | DW | 04.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tada jijiyar wuya tsakanin kasashen EU

Kungiyar Tarayyar Turai na fiskantar matsalar rarrabuwar kawuna bisa yadda za su tsugunar da 'yan gudun hijira.

A taron da ministocin harkokin cikin gidan kungiyar EU suka gudanar sun sanar da batun rarraba 'yan gudun hijira tsakanin kasashe mambobi, wanda zai zama na dindindin ga 'yan gudun hijiran a ko wace kasa da aka tura su. To sai dai batun raba 'yan gudun hijiran na fiskantar adawa daga wasu kasashen EU. Inda ministan cikin gidan kasar Polan Mariusz Blaszczak, ya bayyana cewa matakin fa ba shi da kan gado.

"Wannan mummunan tsari ne. Na farko dai tsarin ya ce rarrabawar ta dindindin ce. Wato a rika kasa 'yan gudun hijira tsakanin mambobin EU, ko wace kasa a bata kasonta. Wannan zance ne marar kan gado. Wato me suke nufi, ma'ana kasar da ba za ta karbi 'yan gudun hijira ba, sai ta biya kudi. Wannan ai zancen banza ne kawai. Ni a madadin al'ummar kasar Polan ina cewa tsarin ba mai karbuwa ba ne."