1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tabrbarewar harkokin tsaro a kasar Afghanistan.

Jamilu SaniMay 6, 2004

Masu lura da alamuran yau da kulum sun sufanta kasar Afghanistan a matsayin kasa kamar irin ta Iraqi,ta la'akari da yadda harkokin tsaro ke kara tabarbarewa a wanan kasa.Masana harkokin yau da kulum sun baiyana cewa rashin tabas din zaman lafiya da ake fuskanta a kasar Afghanistan ya sanya ana sufantata kamar kasar kasar Iraqi,domin kuwa a halin da ake ciki duk kuwa da cewa dakarun Amurka da kuma na sauran kasahen yammacin turia na mamaye da kasar ta Afghanistan,an cigaba da fusakantar matsaloli na tashe tashen hankula,inda aka baiyana cewa yan Taliban sun cigaba azbtar da sojin taron dangi na Amurka tare kuma da kashe su a koda yaushe. Cikin nazarin da masu lura da alamuran yau da kulum suka yi game da harkokin tsaro a kasar Afghanistan

https://p.dw.com/p/Bvjt
Dakarun ketare a Afghaniistan.
Dakarun ketare a Afghaniistan.Hoto: AP

,sun yi nuni da cewa babu wasu alamu na cigaba da ake samu a wanan fuska,a sabili da haka ne suka yi hasashen cewa bisa ga dukanin alamu lamarin harkokin tsaro a kasar Afghanistan zai cigaba da tabarbarewa ne,kamar dai yadda harkokin na tsaro ke kara shiga cikin wani irin mawuyacin hali a kasar Iraqi. Kamar dai yadda yan sari kanoke ke kai hari sojojin taron dangi na Amurka da kuma yan sanda da makatan bada agaji na kasahen duniya a kasar Iraqi,irin wanan hali ne ke afkuwa a halin yanzu a kasar Afghanistan. A lokacin da hukumar tsaron Amurka ta Pentagon ke mayar da martani game da zargin da ake yiwa sojin Amurka dake tozarta fursinonin kasar Iraqi,Pentagon din ta hakikanci cewa fursinoni 25 suka mutu a lokacin da suke tsare a hanun jami’an tsaron Amurka a kasar Iraqi da kuma Afganistan. Da yake gudanar da ziyarar aiki a kasar a Kabul baban birnin kasar ta Aghanistan shugaban hasfsan sojojin Amurka janar Richard Myers,yayi karin hasken cewa mai yiwa ne gwamnati a birnin washington ta dauki matakai na rage yawan sojinta 15,500 da aka tura kasar Aghanistan sanu a hankali da zarar dai an kamala baban zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a kasar Afghanistan watan Satumba mai zuwa. James Ingalls na tsangayar nazarin kimiya da fusaha a jami’ar California,ya baiyana cewa matukar dai Amurka ta dauki matakai na rage yawan dakarunta a kasar Afghanistan,bayan da aka gudanar zaben shugaban kasa,to kuwa na iya nunawa a fili irin fargabar da dama daga cikin alumar Afghanistan keda ita cewa manufar Amurka ba wai ta kyauta samar da cigaban kasa ko kuma rayuwar alumar kasar ta Afghanistan face tabatar da ganin cewa Hamid Karzai ya sake darewa kann karagar mulkin Afghanistan,inda hakan ke nuni da cewa Amurka ta sami nasarar cin nasarar yakin data sanya a gaba na yaki da aiyukan tarzoma data sanya a gaba a duniya baki daya. Ingalls dake zaman daractan da ya taimaka wajen kafa wasu kungiyoyin mata na Afghanistan,ya baiyana cewa yana mai shakun cewa gwmnatin Hamid Karzai zata gudanar da adalci a lokacin da za’a gudanar da sabon zaben da aka dage gudanar da shi daga watan Yuni zuwa watan Satumba na wanan shekara da muke ciki. Mark Sedra wani jami’in bincike a cibiyar nazarin alamuran duniya dake birnin Bonn na nan Jamus dake jagorantar wani shiri na irin cigaban harkokin tsaron da ake samu a kasar Afghanistan,yana mai fatan cewa za’a sami cigaba na harkokin tsaro nan bada jimawa ba a kasar ta Afghanistan. Tun bayan kisan da aka yiwa maikatan bada agaji watan Nuwamban da ya gabata a kasar Afghanistan,kungiyoyin bada agaji na kasahen duniya fiye da 30 suka janye maikatan su daga kudanci da kuma gabashin kasar Afghanistan. A sabili da haka ne majalisar dikin duniya ta dakatar da bada taimako na jin kai ga yan gudun hijirar Afghanistan dake komawa gida daga Pakistan. Masana harkokin yau da kulum sun sufanta kasar Afghanistan kamar kasar Iraqi,ta la'akari da yadda harkokin tsaro ke kara tabarbarewa a wanan kasa.

Masana harkokin yau da kulum sun baiyana cewa rashin tabas din zaman lafiya da ake fuskanta a kasar Afghanistan ya sanya ana sufantata kamar kasar kasar Iraqi,domin kuwa a halin da ake ciki duk kuwa da cewa dakarun Amurka da kuma na sauran kasahen yammacin turia na mamaye da kasar ta Afghanistan,an cigaba da fusakantar matsaloli na tashe tashen hankula,inda aka baiyana cewa yan Taliban sun cigaba azbtar da sojin taron dangi na Amurka tare kuma da kashe su a koda yaushe.

Cikin nazarin da masu lura da alamuran yau da kulum suka yi game da harkokin tsaro a kasar Afghanistan,sun yi nuni da cewa babu wasu alamu na cigaba da ake samu a wanan fuska,a sabili da haka ne suka yi hasashen cewa bisa ga dukanin alamu lamarin harkokin tsaro a kasar Afghanistan zai cigaba da tabarbarewa ne,kamar dai yadda harkokin na tsaro ke kara shiga cikin wani irin mawuyacin hali a kasar Iraqi.

Kamar dai yadda yan sari kanoke ke kai hari sojojin taron dangi na Amurka da kuma yan sanda da makatan bada agaji na kasahen duniya a kasar Iraqi,irin wanan hali ne ke afkuwa a halin yanzu a kasar Afghanistan.

A lokacin da hukumar tsaron Amurka ta Pentagon ke mayar da martani game da zargin da ake yiwa sojin Amurka dake tozarta fursinonin kasar Iraqi,Pentagon din ta hakikanci cewa fursinoni 25 suka mutu a lokacin da suke tsare a hanun jami’an tsaron Amurka a kasar Iraqi da kuma Afganistan.

Da yake gudanar da ziyarar aiki a kasar a Kabul baban birnin kasar ta Aghanistan shugaban hasfsan sojojin Amurka janar Richard Myers,yayi karin hasken cewa mai yiwa ne gwamnati a birnin washington ta dauki matakai na rage yawan sojinta 15,500 da aka tura kasar Aghanistan sanu a hankali da zarar dai an kamala baban zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a kasar Afghanistan watan Satumba mai zuwa.

James Ingalls na tsangayar nazarin kimiya da fusaha a jami’ar California,ya baiyana cewa matukar dai Amurka ta dauki matakai na rage yawan dakarunta a kasar Afghanistan,bayan da aka gudanar zaben shugaban kasa,to kuwa na iya nunawa a fili irin fargabar da dama daga cikin alumar Afghanistan keda ita cewa manufar Amurka ba wai ta kyauta samar da cigaban kasa ko kuma rayuwar alumar kasar ta Afghanistan face tabatar da ganin cewa Hamid Karzai ya sake darewa kann karagar mulkin Afghanistan,inda hakan ke nuni da cewa Amurka ta sami nasarar cin nasarar yakin data sanya a gaba na yaki da aiyukan tarzoma data sanya a gaba a duniya baki daya.

Ingalls dake zaman daractan da ya taimaka wajen kafa wasu kungiyoyin mata na Afghanistan,ya baiyana cewa yana mai shakun cewa gwmnatin Hamid Karzai zata gudanar da adalci a lokacin da za’a gudanar da sabon zaben da aka dage gudanar da shi daga watan Yuni zuwa watan Satumba na wanan shekara da muke ciki.

Mark Sedra wani jami’in bincike a cibiyar nazarin alamuran duniya dake birnin Bonn na nan Jamus dake jagorantar wani shiri na irin cigaban harkokin tsaron da ake samu a kasar Afghanistan,yana mai fatan cewa za’a sami cigaba na harkokin tsaro nan bada jimawa ba a kasar ta Afghanistan.

Tun bayan kisan da aka yiwa maikatan bada agaji watan Nuwamban da ya gabata a kasar Afghanistan,kungiyoyin bada agaji na kasahen duniya fiye da 30 suka janye maikatan su daga kudanci da kuma gabashin kasar Afghanistan.

A sabili da haka ne majalisar dikin duniya ta dakatar da bada taimako na jin kai ga yan gudun hijirar Afghanistan dake komawa gida daga Pakistan.