Tabbatar da tsige shugabar Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 10.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tabbatar da tsige shugabar Koriya ta Kudu

Kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu ta amince da matakin tsige Shugaba Park Geun-hye daga madafun iko bisa badakalar cin hanci.

Cikin wani yanayi na tarihi kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu ta amince da matakin tsige Shugaba Park Geun-hye daga ofis sakamakon badakalar cin hanci da rashawa da aka bankado. Daukacin mambobin kotun sun amince da matakin abin da zai iya share fage na a tuhumi tsohuwar shugaban kasar, wadda take zama shugabar kasa ta farko da aka tsige karkashin tsarin demokaradiya da ake aiki da shi a kasar tun cikin shekarun 1980.

Karkashin dokokin Koriya ta Kudu tilas a shirya zabe cikin watanni biyu domin samun wanda zai gaji Shugaba Park Geun-hye da aka tsige wadda ita ce mace ta farko da ta shugabanci kasar da ke sahun gaba cikin kasashe masu karfin tattalin arziki, kuma tun cikin watan Disamba majalisar dokoki ta tsige shugabar.

Duk wanda zai dauki madafun ikon kasar ta Koriya ta Kudu yana aikin kan dangantaka da Koriya ta Arewa, da farfado da tattalin arziki gami da sasanta 'yan kasa sabakaon rarrabuwan kai, inda yanzu haka magoya bayan tsohuwar shugabar kasar suke zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsige ta daga madafun iko.