Tabbatar da daurin shekaru 50 a kan Taylor
September 26, 2013Kotu ta musamman dake da zama a birnin Hague, wadda ke da goyon bayan Majalisar Dunkin Duniya ta tabbatar da daurin shekaru 50 a kan tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor. A bara ne dai aka yanke wa Taylor mai shekaru 65 da haihuwa, hukuncin zaman gidan kurkuku na shekaru 50, saboda samunshi da taimaka wa kungiyar 'yan tawaye a lokacin yakin basasar kasar Saliyo dake makwabtaka da Liberia.
A yayin da ya ke watsi da karar da Mr Taylor ya shigar gabansa, Alkalin kotun ya ce an yi adalci a hukuncin farko da aka yanke masa. Lauyan tsohon shugaban na Liberia dai, ya nemi kotun da ta soke hukuncin tare da wanke shi, saboda kuskuren da ya ce an samu a lokacin shari'arsa a baya. Sai dai kotu ta yi watsi da bukatun masu shigar da kara na kara wa'adin zaman kurkun daga shekaru 50 zuwa 80.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh