Tabbacin ′yan takara a zaben Faransa | Labarai | DW | 18.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tabbacin 'yan takara a zaben Faransa

Faransa ta sanar da sunayen mutane 11 da suka cika ka'idodin tsayawa takara a shugabancin Faransa da ke tafe.

Kotun tsarin mulkin Faransa ta bayyana sunayen 'yan takara 11 da za su fafata, a zaben shugaban kasa da zai gudana a watannin Afirilu da Mayu. Masu fashin bakin harkokin siyasa sun nunar da cewar biyar daga cikin 'yan takara na iya kai wa zagaye na biyu na zaben, ciki har da 'yar takara daga jam'iyyar FN da ke kyamar baki Marine Lepen, da tsohon ministan tattalin arziki a wannan gwamnatin Emmanuel Macron da tsohon firaminista kuma dan takarar jam'iyyar LR da ke da ra'yin rikau Francois Fillon, sai dan takarar jam'iyya mai mulki Benoit Hamon da kuma na masu matsakaicin ra'ayin gurgurzu Jean Luc Mélenchon.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a baya-bayan nan ta nunar da cewar Marine Lepen da ke kyamar baki za ta zo ta daya a zagayen farko na zaben Faransa, yayin da tsohon ministan tattalin arziki kana shugaban kungiyar En Marche mai shekaru 39 Emmanuel Macron zai yo na biyu. Sai dai kuma Macron zai iya doke ta a zagaye na biyu saboda goyon baya da zai samu daga sauran 'yan takara.