1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tabargazar Visa A Ofisoshin Jakadancin Jamus

Ana zargin ma'aikatan ofisoshin jakadancin Jamus dake ketare da laifukan taka rawa wajen tuttudowar bakin haure zuwa kasar ba a bisa ka'ida ba

Bisa ga ra’ayin manyan jami’an ‚yan hamayya na Christian Union kamata yayi ministan harkokin waje Joschka Fischer yayi murabus daga mukaminsa sannan shi kuma ministan cikin gida Otto Schily ya bi sau. Suka ce babban dalili shi ne damar da aka ba wa dubban daruruwan bakin haure da kuma wasu matan da akan tilasta musu sana’ar karuwanci, wajen malalowa zuwa kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ta kan kasar Jamus a cikin shekarun da suka wuce. An saurara daga bakin Eckhart von Klaeden, babban jami’in Christian Democrats kuma shugaban kwamitin bin bahasin na majalisar dokoki yana mai ikirarin cewar Joschka Fischer na da cikakkiyar masaniya a game da abin dake faruwa amma yayi ko oho da lamarin. A cikin watan maris na shekara ta 2000 Jamus ta gabatar da wata sabuwar manufa ta ba da izinin shigowa kasar, wacce ta tanadi ba da la’akari da ‚yancin tafiye-tafiye wajen ba da visa. ‚Yan hamayya suka ce wannan manufa ta bude kofofi da gwamnatin Schröder ta gabatar ta taimaka ‚yan baranda a kasashen gabashin Turai suka samu wata dama karbar makudan kudade daga hannun mutanen dake sha’awar shigowa kasashen Kungiyar Tarayyar Turai. Misali a kasar Ukrain an samu bunkasar yawan mutanen da ake ba su visar shigowa Jamus a matsayin ‚yan yawon bude ido, daga mutum dubu 133 a shekarar 1998 zuwa mutum dubu 300 a shekara ta 2001. A tsakanin wadannan mutanen akwai akalla wasu guda biyu da ake tuhumarsu da kasancewa ‚yan ta’adda, wadanda ke da hannu a matakin garkuwa da mutanen da aka yi a wani gidan wasan kwaikwayo dake birnin Mosko a shekara ta 2002, in ji jami’in siyasar na jam’iyyar Christian Democrats. Rahotanni sun ce ministan cikin gida Otto Schily ya dade yana mai gargadi a game da yadda aka yi wa al’amuran shige-da-ficen rikon sakainar kashi. A jiya alhamis dai wakilan jam’iyyun SPD da the Greens a kwamitin bin bahasin sun ki amincewa da bukatar da aka gabatar da neman ministan harkokin waje Joschka Fischer da ya ba da shaida gaban kwamitin kafin wani muhimmin zabe na jiha da za a gudanar a cikin watan mayu mai zuwa. Shi kansa ministan harkokin wajen na Jamus dai har yau bai ce komai ba, bayan bayyanar da yayi a gaban kwamitin ranar litinin da ta wuce, inda yayi kokarin mayar da tabargazar tamkar wani abin ba’a. Amma fa ‚yan hamayya sun dage akan lalle sai Fischer ya sauka daga kan mukaminsa, musamman bayan da wani daya daga cikin jami’an ma’aikatarsa yayi murabus ranar makon da ya wuce. ‚Yan hamayyar so suke yi su yi amfani da wannan dama domin samun goyan baya a zabubbukan jihohin da za a gudanar a ranar lahadi da kuma karshen watan mayu mai zuwa, kazalika da zaben majalisar dokoki a shekara ta 2006.