Tabarbarewar rayuwa jamaá a Somalia | Labarai | DW | 25.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tabarbarewar rayuwa jamaá a Somalia

Hukumomin bada agaji na kasa da kasa sun sanar da cewa halin da ake ciki na yanayin rayuwar alúma a Mogadishu babban birnin Somalia yayi muni matuka. Dubban jamaá wadanda ke tsananin bukatar ruwan sha da kuma abinci na ta yin kaura saboda sake barkewar fada tsakanin sojojin Somalia dake da goyon baya daga dakarun kasar Habasha da kuma yan kotunan Islama. Kungiyar agaji ta Medicenes San Frontiers tace akwai yiwuwar barkewar cutar kwalara da wasu cutattukan a sansanonin da aka tanada domin tsugunar da yan gudun hijirar. Wani babban jamiín majalisar dinkin duniya yace fadan da ake yi yanzu a Somalia shi ne mafi kazanta a tsawon shekaru goma sha shida da suka wuce. A halin da ake ciki Amurka ta yi kra da tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar gamaiyar Afrika domin maye gurbin sojojin Habasha domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar. Kakakin fadar white House Sean M´cCormack yace Amurkan bata bukatar ganin an sami gibi a yayin da sojin Habasha´n za su janye daga Somalia.