Tabarbarewar harkokin tsaro a Iraqi | Labarai | DW | 02.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tabarbarewar harkokin tsaro a Iraqi

Wasu masana ilimin harkokin leken asiri a Amurka sun bayana halin da Iraqi ke ciki a matsayin mawuyacin hali, sakamakon rashin doka da kuma oda.

Masanan sun kuma yi gargadin cewa matukar ba´ayi hankali ba,

rikicin da Iraqi ke fuskanta ka iya daukar wani sabon salo.

Masanan sun fadi hakan ne a cikin wani rahoto da suka fitar yau, inda suka ba da misali da yadda hare haren sari ka noke dana kwanton bauna ke kara kazanta , duk kuwa da matakan tsaron da ake ci gaba da dauka.

Bugu da kari rahoton ya kuma yi tsokaci da cewa janyewar dakarun sojin Amurka daga kasar, ka iya haifar da tabarbarewar harkokin tsaro a Iraqin.

Wannan sabon rahoto dai yazo ne a dai dai lokacin da a tsawon mako guda daruruwan mutanwe a Iraqi suka rasa rayukan su, wasu kuma da dama suka jikkata.

Idan dai an iya tunawa a farko farkon watan janairun wannan shekarar ne shugaba Bush na Amurka yace zai tura karin dakarun soji dubu 21 da dari biyar izuwa kasar ta Iraqi.