1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe(19.04.2017)

Gazali Abdou Tasawa
April 20, 2017

Shirin na dauke da bayani kann bukin kaddamar da sabon kundin wakoki na shahararren mawakin Abzinawa na kasar Nijar Alhousseini Anivolla wanda aka yi a farkon watan Aprilu a birnin Berlin na Jamus

https://p.dw.com/p/2bbCp

A shekarun baya malam Alhousseini Anivolla wanda makadin guitar kana mawaki ya kasance a cikin Kungiyar Etran Finatawa shahararriyar kungiyar gambizar makadan Abzinawa da filani ta kasar Nijar, kafin daga bisani ya koma yin aiki shi kadai. Kuma wannan  sabon kundin waka mai suna OSAS shi ne kundin waka na biyu da ya buga shi kadai. To sai dai kuma wannan shi ne karo na farko da ya kaddamar da albun din wakokinsa a kasar Jamus.