1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: (30.+31.12.2015)

January 3, 2016

An jaddada cewa kafofin yada labarai na daga cikin manyan kafofi masu isar da sakonni ga al'umma da gudunmawarsu take da mahimmanci.

https://p.dw.com/p/1HXMb

Hukumar masu fassara da tafinta ta Najeriya ta yaba da gudunmawar da kafofin yada labarai ke bayarwa wajen fassara sakonnin da ake bukatar su isar ga al'umma. Hukumar ta yi wannan yabo ne a lokacin babban taronta da masu ruwa da tsaki a harkar fassara da tafinta daga bangarori daban-daban suka halarta wanda kuma a karon farko Jami'ar Bayero da ke Kano ta dauki bakoncinsa.