1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 28.03.2018

Mohammad Nasiru Awal
March 29, 2018

Gagarumin shirin Shugaba Macron na bunkasa harshen Faransanci ya zama daya daga cikin manyan harsuna na duniya.

https://p.dw.com/p/2vDRo

A kwanakin baya ne shugaba Emmuel Macron na Faransa ya kaddamar da wani shiri mai cike da babban buri da nufin mayar da harshen Faransanci daya daga cikin manyan harsuna na duniya musamman ma a nahiyar Afirka da ke zama gida ga mafi akasarin masu amfani da harshen na Faransanci.

Sai dai yayin da wasu masu kishin harshen Faransanci ke yaba wa shirin da aka ware kudi na miliyoyin Euro don bunkasa harshen Faransanci, masu sukar lamiri musamman 'yan Afirka sun ce shirin na da wata manufa ta sabon salo na mulkin mallaka.