Taba Ka Lashe: 22.+23.06.2016
June 24, 2016Talla
A yayin da aka shiga kwanaki goma na tsakiyar watan Ramadan, a wasu jihohin arewacin Najeriya har ma da Jamhuriyar Nijar, lokaci ne na raya al'adar tashe da nufin nishadantar da masu azumi. Sai dai wannan al'ada ta fara fuskantar komabaya a wasu yankunan na kasar bisa dalilai dabam-dabam.