1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 17.+18.02.2016

February 19, 2016

Sarakunan gargajiya a yankin Bambey da ke a jihar Tahoua ta Jamhuriyar Nijar sun dukufa a kokarin farfado da al'adun gargajiyar al'ummar wannan yanki.

https://p.dw.com/p/1HygX

A wani matakin farfado da al'adun gargajiya da ke neman dushewa biyo bayan watsi da al'umma ta yi da su, a jamhuriyar Nijar wasu magadan gargajiya ne irin su sarakuna ke yunkurin maido da martabar al'adun domin nuna wa matasa irin muhimmancinsu ga rayuwar yau da kullum. A kan haka ne a kwanakin baya a yankin Bambey na jihar Tahoua aka gudanar da wasannin gargajiya da ake wa lakabi Sarho.