Taba Ka Lashe: (11.+12.11.2015)
November 13, 2015Talla
Kungiyar ta bayyana kudirin na ta ne a lokacin wani babban taronta a Kano a inda mawakan addini da dama a Najeriya suka hallara. Ita dai wannan kungiya ta Jama'atu shu'ara'il Islam ta Najeriya wadda ta kunshi mawakan yabon Annabi Muhammad da ma sauran al'amuran addinin Musulunci ta yi alkawarin ba da gudunmowar 'ya'yanta a gwagwarmayar da mahukuntan Najeriya ke yi wajen samar da zaman lafiya a kasar.