1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 09.05.2018

Abdullahi Tanko Bala MNA
May 14, 2018

Baje kolin zane-zanen tarihin Afirka da cigabanta a garin Bayreuth a Jamus.

https://p.dw.com/p/2xgBD

Taken baje kolin dai shine waiwayen Afirka a shekarun 1980 ta mahangar masu fasahar zane a Afirka da kuma masu zane 'yan Afirka da ke zaune a kasashen waje.

Cibiyar tarihi ta Iwalewa karkashin jami'ar Bayreuth da gidan adana kayan tarihi Weltkulturen Museum da ke Frankfurt a nan Jamus da kuma Jami'ar Makerere da ke Kampala a Yuganda su ne suka hadu suka jagoranci gudanar da wannan baje koli.

Babban makasudin baje kolin shi ne fahimtar yadda masu zane zane ta hanyar hikima da baiwar da Allah Ya hore musu suka yi kokarin fito da muhimman abubuwan da suka faru a Afirka a shekarun 1980.