Taba Ka Lashe: 08.+09.06.2016
June 10, 2016Talla
A Kamaru, Islama na daga cikin manyan addinai biyu da 'yan kasar ke bi. Sa dai hare-hare daga tsagerun Boko Haram a yankin arewacin kasar da ya kunshi dimbin musulmi ke fama da su, ya sa shugabannin addini zabura, don hana amfani da wannan dama wajen raba kawunan Musulmi. Saboda haka ne suka dauki matakan horas da Limamai tare da tsara wa'azi a masallatai domin kauce ma fadawa cikin kaifin kishin addini.