Taba Ka Lashe: 08.02.2017 | Al′adu | DW | 10.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Al'adu

Taba Ka Lashe: 08.02.2017

Wasannin motsa jiki tsakanin matasa Musulmi da Kirista da masu bin addinan gargajiya a wani mataki na karfafa zamantakewa tsakanin al'umma.

Malaman addinai da kungiyoyin farar hula da ke fafutukar tabbatar da zaman lafiya a Najeriya na ci gaba da shirya wasannin motsa jiki tsakanin matasa Musulmi da Kirista da masu bin addinan gargajiya a wani mataki na karfafa zamantakewa tsakanin al'umma. A Kaduna da ka arewacin Najeriya an shirya irin wannan wasan motsa jiki don kara fahimtar juna tsakanin al'ummar wannan jiha da ta yi suna wajen fama da tashe tashen hankula masu nasaba da addini.

Sauti da bidiyo akan labarin