Taba Ka Lashe: 07.12.2016
December 9, 2016Talla
Sashen harsuna da al'adun Afirka na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a arewacin Najeriya ya tattaro kwararrun masana harshen Hausa inda suka gudanar da taro kan inganta harshen Hausa da ma duba sabbin hanyoyin karantarwa don bunkasa harshen na Hausa da kuma kare shi daga gurbacewa.