1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 01.02.2017

Mohammad Nasiru Awal
February 3, 2017

'Yan gudun hijirar da matsalar sanyin hunturu a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/2Wvqq

A kwanakin nan ana fama da sanyin hunturu mafi tsanani cikin shekaru gommai a kasar Sabiya. Amma a bayan tashar jirgin kasa da ke a tsakiyar birnin Belgrade sama da 'yan gudun hijira dubu daya ne ke jure wa sanyin na hunturu a wasu tsoffin gine-ginen ajiye kaya ba tare da sun samu wani taimako ko injin dumama daki ba. Su dai 'yan gudun hijihar suna fatan ci gaba da tafiya zuwa yammacin Turai, amma mahukuntan Hungary da Kuretiya sun hana su tsallake kan iyakokinsu, saboda haka suka makale a Belgrade.