1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'azzarar da tsaro ke yi a Najeriya

Abdullahi Maidawa Kurgwi
April 27, 2018

Jami'an tsaro a Najeriya sun ce suna kan kokarin shawo kan matsalar da tayi kamari a jihar Benuwe, bayan-kashe kashen rayukan jama'a da ke ci gaba da wakana a jihar sakamakon rikicin makiyaya da manoma.

https://p.dw.com/p/2woR2
Nigeria - Boko Haram
Sojojin Najeriya na aikin samar da tsaroHoto: picture-alliance/dpa

Wannan matsala ta tsaro a jihar Benuwe dai ta soma zarce tunanin jama'a, don kuwa ko a makon nan kawai an kashe mutane fiye da 70, don ko baya ga harin ranar Talata a kauyen Mbalong na yankin Gwer East, da kuma wanda aka yi washe garin Laraba a wasu kauyuka da ke yankin Guma. A birnin Makurdi da kewaye ma, a yammacin Laraba an yi hasarar rayuka, kana a ranar Alhamis a yankin Mbamondo da ke gundumar Gambatie cikin karamar hukumar Logo, shi ma ya fuskanci sabbin hare-haren da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 da aka ce suna neman mafaka a wata Majami'a.

Nigeria Menschenhandel | Naka
Hoto: DW/K. Gänsler

Koda yake a garin Makurdi a nan iya cewa al'amuran sun soma sauki, majiya ta ce matasa 'yan arewa da ke kananan sana'o'i suna dari-darin shiga wasu wurare a garin. To sai dai da alamu matsalar tsaron tafi kamari ne a  kauyukan dake kananan hukumomin jihar.

 

Shugaban hukumar agajin gaggawa na jihar Benue Emmanuel Sheo, ya ce babu wani abin da ya sauya duk da zuwan sojoji, don tamkar zuwan su a cewarsa ya kara dagula lamura ne. 

A galibin lokuta dai a kan dora laifin kashe-kashen ne kan fulani makiyaya inda kuma su fulanin ke zargin 'yan sintiri da gwamnan jihar ya kaddamar don sa ido kan dokar hana kiwo. Tuni dai hadin gwiwar majalisar tarayyar Najeriya ya bukaci shugaba Buhari da ya bayyana gabansa don yin bayani kan wannan rikici na jihar Benue da ma wasu da ke wakana a wasu sassa na kasar.