1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'addanci: Masar ta soki kasashen duniya

Ahmed SalisuAugust 19, 2015

Mahukuntan Masar sun yi suka da kakkausar lafazi ga kasashen duniyar da suka yi Allah wadai da sabuwar dokar yaki da ta'addanci da aka amince da ita a cikin wannan makon.

https://p.dw.com/p/1GHu7
Ägypten Präsident al-Sisi
Hoto: Getty Images/Afp/K. Desouki

Ma'aikatar harkokin wajen Masar din ta ce tsoma baki da kasashen suka yi katsalandan ne a harkokinta na cikin gida da kuma rashin mutunta bangaren shari'ar kasar.

Ma'aikatar ta ce ko kusa Masar ba ta sanya bakinta a kan dokokin yaki da ta'addanci da wasu kasashen su ka amince da su duk kuwa da cewar suna da matsaloli iri-iri, don haka ba ta ga hujjar tsoma baki a nata harkokin ba.

Kasashen da ke sukar wannan sabuwar doka ta Masar ciki kuwa da Amirka da wasu kungiyoyi na kare hakkin bani Adama na fargabar dokar za ta iya keta hakkin dan Adam da kuma muszgunawa kafafen watsa labarai.