Ta leƙo ta koma: garambawul a gwamnatin Guinee-Conacry | Labarai | DW | 05.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ta leƙo ta koma: garambawul a gwamnatin Guinee-Conacry

A yammacin jiya ne, shugaban ƙasar Guinee Konacry,Lansana Konte, ya yi gagaramin garambawul ga gwamnatin sa.

A cikin wanan garambawul, ya sallami ministoci 12, sannan ya ƙarffafa muƙamin Praminista, Cellou Dalein Diallo.

Daga yanzu, kujerun ministocin kuɗi, da na passal,i da tattalin arziki, da kuma ministan harakokin waje, duk sun dawo ƙarƙashin mulkin Praminista.

Sabin ministoci 13 su ka shigo a cikin gwamnatin.

Wannan Garambawul, ya biwo bayan kwanaki ƙalilan, da Shugaban ƙasar,ya dawo daga ƙasar Suizland, inda ya yi jiya a assibiti.

A nasu ɓanagare yan adawa, na bayyana bukatar su, ta girka gwamnatin riƙwan ƙwarya, ta la´akari da yadda shugaban ƙasa Lansana Konte,ya zama je ka na yi ka, dalili da matasanciyar rashin lahia da ya ke fama da ita, a tsawan shekaru da dama.

To saidai a wani mataki na bata shugaba Konte ya lashen amen sa, bayan da sojoji su ka tada borin kin amincewa da wannan garamabawul.