1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taɓargaza a hukumar FIFA

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya na binciken wani jami'in Najeriya, bisa zargin sayar da ƙuri'arsa.

default

Joseph Sepp Blatter shugaban hukumar FIFA.

Hukumar kwallon ƙafa ta duniya wato FIFa tace tana binciken labarin da wata jaridar Birtaniya ta wallafa, wanda yace wasu jam'ian hukumar sun nemi sayar da ƙuri'unsu a lokacin zaɓen ƙasar da za ta dauki nauyin gasar cin kofin duniya wanda ya gabata. Jaridar Sunday Time ta Birtaniya ta ce, jam'ian wato waɗanda suka haɗa da Amos Adamu na Najeriya da Renald Temarii na Tahiti anji suna tambayan kuɗi don gudanar da wasu ayyuka. An dai zargi mutanen da cewa sun buƙaci kamfanonin Amirka da su bayar da na goro, a yunƙurin ƙasar Amirka na sake ɗaukar nauyin ƙasar wanda ta nema.

Bayanai sun tabbatar da cewa Amos Adamu na Najeriya ya jefawa Amirka ƙuri'arsa kuma an yaɗa wani faifayin vidiyo, inda aka ji Amos Adamu yana tambayar kamfanonin Amirka kuɗi, kowannensu ya nemi dalar Amirka fiye da miliyan ɗaya da rabi idan ana son ƙuri'arsa. Tuni dai shugaban hukumar ƙwallon ƙafan Amirka yace amma dai jaridar bata ambaci ko ƙungiyasa ce ke da hannu ba.

Wannan badaƙalar dai ta faru ne a zaɓen ƙasar da za ta ɗauki nauyin ƙasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya a shekara ta 2018. Jaridar Sunday Time tace wasu 'yan jarida da suka yin sojan gona, suka ce su wakilan kamfanonin Amirka ne, sun samu Amos Adamu dake wakilitar Najeriya da kuma wani jami'in Oceniya, inda suka buƙaci da sai a basu dalar Amirka miliyan ɗaya da dari shida, idan dai ana son ƙuri'arsu, ba tare da sanin cewa 'yan jaridan na naɗar bayanan da waɗannan jam'an suke yi. Hukumar FIFA dai tace tana son a bata faifayin vidiyon don ta yi natsari a kai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu