Taɓarɓarewar tsaro a Iraƙi | Siyasa | DW | 05.11.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taɓarɓarewar tsaro a Iraƙi

Al'amuran tsaro na daɗa taɓarɓarewa kusan a kullu yaumin, lamarin dake jefa al'umar ƙasar cikin mawuyacin hali game da makomar rayuwarsu

default

Taɓarɓarewar al'amuran tsaro a Iraƙi

Watanni uku bayan janyewar dakarun Amurka daga manyan biranen ƙasar Iraq, har yanzu halin da ake ciki na rashin tsaro a ƙasar bai inganta ba. Kusan a kullum sai an kai hare hare da ke halaka mutane da dama. Farin cikin farko bayan sanar da janyewar dakarun na Amurka, yanzu haka ya kau a yankuna da dama, a maimakon haka zai zaman zulumi da fargabar hare hare.

"halin da ake ciki a Iraki ya inganta, yanzu haka tashe tashen hankula sun ragu"

A duk lokacin da shugaba Obama ya fito gidan TV yana faɗin haka, hankulan 'yan ƙasar Iraqi kan rabe tsakanin bacin rai hakuri ko fidda tsammani. Tun janyewar sojojin na Amurka daga manyan biranen Iraki, sojojin ne kadai suke cin moriyar raguwar tashe tashen hankula ko raguwar kai hare hare akansu, ga fararen hula na Iraki kuwa, wadanda jami'an tsaron kasar suka karbi ragamar kare su, rayuwarsu na cikin hadari fiye da a baya.

Cikin hare hare a arewacin babban birnin kasar, a yankunan Kirkuk da kuma Mosul, bugu da kari kuma da birnin Baghdad din kansa, mutane fiye da 150 suka halaka a ranar Lahadi ta karshen watab Oktoba, fiye da 100 kuma a tsakiyar watan Agusta, bala'o'i da mazauana manyan biranen ke fuskanta ke nan, abin kuma da ya tayarwa tare da taba hankalin jama'ar yankunan.

"hare hare a kadayaushe, da yawa su mutu, ba shakka muna cikin fargaba, duk inda mutum zai je, dole ne kayi tunanin haka"

Haka mafi yawan mazauna birnin Bagadaza suke gani kamar wannan 'yar talika, wannan fargaba tana nan, duk kuwa da ikrarin da gwamnati ke yi cewa ta daidaita komai. A hakikanin gaskiya dai a watan Oktoba an kashe mutane da dama kusan ribi biyu na wadanda aka kashe a watan Satumba. Babu shakka tun da Amurkawa suka koma baya, babu wani tsaro da ya inganta a kasar. kamar yadda mafi yawan jama'a ke cewa.

"Dawowar tashe tashen hankula da fashe fashen bam tare da rawar da sojin Amurka ke takawa suna da alaka kai tsaye. Ba zai yiwa shugabanninmu dadi ace dakarun Amurka sun bar kasar gaba daya ba, saboda rayuwarsu ta dogara ne kacokan kan sojojin Amurkan"

Mutane 410 suka halaka cikin hare hare a watan Oktoba, idan an kwatanta da 203 a watan Satumba, a watan Juli mutum 275, yaiynda mutane 456 kuma a watan Agusta, tun lokacinda sojin Amurkan suka janye, batun tsaro baya a hannun sojoji ko 'yan sandan Iraki, maimakon haka yana a hannun masu kai hare haren ne.

Dukkaninsu rundunonin sojin Amurka da na Iraki suna fargabar cewa sabbin hare hare zasu iya kawo cikas ga zabe da aka shirya gudanarwa a watan Janairu ko kuma ma hana zaben baki daya.Abinda kuma zai iya jefa kasar cikin sabon rikici. Firaminista Nuri al Maliki ya karbi mulki ne don ya tabbatar da tsaro a kasar, to sai dai masu adawa da tsarinsa suna masa zagon kasa, haka ma 'yan siyasa mazambata suna kokarin kara tsunduma kasar cikin rikici ta yadda 'yan kasar suka fidda tsammani kan komai.

"ba abinda sukeyi sai magana, wannan kuma ba abinda zai haifar"

Amma duk da haka 'yan siyasar Iraki kamar na Amurkan suna ci gaba da nuna cewa halin da ake ciki ya inganta.

Mawallafi: Hauwa Abubakar Ajeje

Edita: Ahmad Tijani Lawal