Taɓa Ka Lashe: 17.02.2010 | Al′adu | DW | 17.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Al'adu

Taɓa Ka Lashe: 17.02.2010

Masana a Najeriya sun gano cewar malaman makarantu masu koyar da harshe ba sa samar da ingantacciyar koyarwa, hakan na haifar da gurɓacewar harshe a cikin al´uma

Wani nazari da masana a tarayyar Najeriya suka yi sun gano cewar malaman makarantu masu koyar da harshe ba sa samar da ingantacciyar koyarwa, hakan na haifar da gurɓacewar harshe a cikin al´uma. Baya ga lalata wasu kalmomi na harshe ko dai a rubuce ko a karance ko kuma wajen furtasu a magana. Wata matsalar kuma ita ce ɗalibai kan kasa cin jarrabawa saboda rauninsu wajen rubutawa ko karanta harshe. A wata bitar da cibiyar Inuwar Jama´ar Kano ta shirya  an bayyana matsalar da rashin fahimtar turanci ke haifarwa ga ɗaliban makarantu musamman saboda a wasu lokutan su kansu malaman ba su goge ba ko kuma ba su fahimci yadda ake faɗan wasu kalmomi daidai ba ko kuma yadda ake gina jimla sai ka ga suna koyarwa ya zamanto gaba ɗaya an tafi akan kuskure.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala

Sauti da bidiyo akan labarin