Taƙaddamar Koriya ta Kudu da ta Arewa | Labarai | DW | 23.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taƙaddamar Koriya ta Kudu da ta Arewa

Sojojin Koriya ta Arewa sun hallaka takwarorinsu na Kudu a wani ɗauki ba daɗi da ya gudana tsakaninsu a kan iyakokin ƙasashen biyu.

default

Dakarun koriya ta Kudu a fagen daga

Sojojin Koriya ta Kudu biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu dakaru da fararen hula suka jikata, a lokacin da takwarorinsu na Koriya ta Arewa suka buɗe musu wuta a wani tsibirin da ke kan iyakokin ƙasashen biyu. Wannan dai shi ne hari mafi muna da Koriya ta Arewa ta kai wa takwararta ta Kudu a cikin shekaru sama da 50 na baya-bayanan da suka shafe suna taƙammada da juna. Awa guda ɓangarorin biyu suka shafe suna misayan wuta tsakaninsu kafin a kwashe mutanen da ke tsugune a tsibirin na Yeong Pyong.

Shugaban Koriya ta Kudun Lee Myung Bak ya kira wani taron gaggawa na majalisar ministocinsa da nufin cimma matsaya game da martanin da ƙasarsa za ta mayar. Tun watanni takwas da suka gabata ne aka fara fiskantar hauhawar ƙamarin tsakanin Koriyoyin biyu ,sakamakon ƙaddamar da murhun inganta makamashin Uranium da Koriya ta Arewa ta yi; da kuma zargin da koriya ta Kudu ta yi wa ta arewa na nitsar da ɗaya daga cikin jiragen ruwanta.

Shugabannin ƙasashen duniya daban daban na ci gaba da neman ƙasashen biyu da sukai hankali nesa. Misnistan harkokin wajen Jamus, wato Guido Westerwelle ya ce duk wata takun saƙa tsakanin koriyoyin biyu za ta iya haifar da rikici a wannan yanki na Asiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala