1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taɓargazar kwamandan NATO

June 23, 2010

Kwamandan sojin Amirka da ruddunar tsaro ta NATO a Afganistan, Janaral McChrystal ya yi murabus, kuma har an maye gurbinsa.

https://p.dw.com/p/O1IA
Janaral Stanley McChrystal da ObamaHoto: AP

Shugaban Amirka Barak Obama ya amince da murabus ɗin da babban kwamangan sojojin Amirka dana NATO a ƙasar Afghanista, Janar Sternley McChrystal. Ɗazunnan ne dai Janar na sojin ya miƙa takardar barin aikin nasa bayan cece kucen daya biyo, Inda shi da muƙarrarabansa su ka yi wasu kalamai akan manyan jami'an gwamnati Amirka cikin wata hirar da suka yi da wata mujallar ƙasar ta Amirka. A yanzu dai shugaba Obama ya amince da naɗin Janar David Petraeus, wanda ya yi fice a jagorantar dakarun Amirka dake yaƙi a ƙasar Iraƙi, domin ya maye gurbin Janar McChrystal, a jagorantar dakarun Amirka dana ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO a ƙasar ta Afghanistan.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal