1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240610 Obama McChrystal Petraeus

June 24, 2010

Gwamnatin Obama ta ɗau tsauraren matakai bisa kalaman kwamandan dakarun ƙawance a Afganistan

https://p.dw.com/p/O1nj
Janaral Stanley McChrystalHoto: AP

Shugaban ƙasar Amirka Barack Obama ya kori babban kwamandan dakarun ƙawance da suke yaƙi a ƙasar Afganistan, bayan da kwamandan wato Janaral Staley McChrystal ya yi wasu kalamai da suka ɓatawa mahukuntan Washington rai bisa yaƙin Afganinstan. Tuni dai Obama ya naɗa David Petraeus a ya maye gurbin Janaral McChrystal.

A watan junin barane dai Obama ya naɗa stohon kwamanda da ya yaƙi masu data ƙayar baya na Iraƙi, wato Janaral Stanley McChrystal, ya kasance babban hafsan dakarun Amirka dake Afganistan. Ɗan shekaru 55 Janaral McChrystal ya maida hankaline wajen taƙaita kisan fafaren hula, kana ya fara neman hanyoyin da za'a samu karɓuwa ga dakarun ƙawance a wajen 'yan Afganistan, Inda a gefe guda ya maida hankali bisa tinkarar 'yan Taliban da sukayi tunga a kan iyakar Pakistan.

Ana masa kallon wani ƙwarrare da iya dabarun yaƙi da 'yan sari ka noƙe. Don haka ma wassu daga cikin 'yan majalisar dokokin Amirka ke cewa, har yanzu basu fahimshi irin saƙon da yake son aikawa ba, bisa kalaman da ya yi a hirarsa da wata jaridar ƙasar ta Amirka. Jaridar Washington Post, ta rawaito cewa ƙasar Pakistan da ma shuagaba Hamid Kaizai sun gargaɗi Obama kan korar mutumin da muƙaminsa yake cike da matuƙar sirri. To Amma bayan yin ido huɗu da Obama ya yi da Janaral McChrystal, ana kamalla zaman da majalisar tsaron ƙasar ta yi, sai Obama yace ya amince da murabus ɗin Janar ɗin, kuma yana farin cikin sanar da David Petraeus a matsayin wanda ya maye gurbin, inda yace

"Na ɗau wannan matakinne bawai domin akwai wassu bambance bambancen da muke dasu, a manufar da muke da ita a Afganistan ba, sai dai kwai tsarinmune da muka amince da shi. Ba wani abune da ya haɗa mu ba, Janarl McChrystal yana biyayya kuma yana aiwatar da da umarnin da nake bashi"

Duk da cewa Obama ya yi kalaman jinjinawa Janaral ɗin da ya kora, to amma ya kwatanta kalaman da McChrystal ya yi da cewa, taɓargazace kwamandan soji ya yi furta irinsu a jaridar Rollin Stone, kuma a cewar Obama rashin girmama ikon da farar hula ke da su ne. kamar yadda yaci gaba da cewa

"Irin halaye na kalaman da aka wallafa a jaridar, basu da makama. kuma basu kamaci su fito daga wani babban hafsan soji ba, kana wani cin fiskane a ikon da farar hula ke dasu kan sojoji, a tafiyarmu ta siyasa. Hakan ya raunata amanar dake tsakaninmu, a manafarmu ta yaƙin Afganistan"

Koma dai waɗannen dalailai ne suka sa janaral McChrystal sukar ƙusoshin gwamnatin ƙasar sa ta Amirka, baza a fito fili aka yiwa mutane bayani ba, sai dai wata ƙila, a ganawar da suka yi bayan ido, ya shaidawa shugaba Obama dalilansa na ɗaukar wannan mataki, na tsile Amirkawa a bainal jama'a.

 Matakan ba sassaucin da Obama ya ɗauka, sun samu karɓuwa daga aksarin sanatocin ƙasar, kuma zaɓar David Petaeus suka ce ya yi, domin tun a shekara ta 2008 yake jagorantar dakarun Amirka a Iraƙi, waɗanda acanma dai kusan Afganistan ɗinne, inda ake karawa da masu tada ƙayar baya.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Silke Hasselmann

Edita: Umaru Aliyu