1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taɓa Ka Lashe: 28.04.2010

April 29, 2010

Sabuwar jam'iyar Musulmai a Jamus BIG na fatan taka rawar gani a fagen siyasar ƙasar

https://p.dw.com/p/N9M9

A karon farko sabuwar jam'iyar Musulman mazauna Jamus mai sunan BIG a taƙaice, za ta tsaya takara a zaɓen 'yan majalisar dokokin jihar North Rhein Westfaliya da za a yi a ranar 9 ga watan Mayu. Jam'iyar ta ƙuduri aniyar gabatar da abin da ta kira siyasa ta zahiri a Jamus.