1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taɓa Ka Lashe: 24.02.2010

February 25, 2010

Bikin nuna fina-finai na Berlinale a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/MAxl

Bikin na bana dai shi ne karo na 60, kuma an mayar da hankali kan fina-finai na addinai da zamantakewa daga cikinsu kuwa da wani fim mai taken Shahada da wani daraktan shirya fina-finai ɗan Jamus mai asali da ƙasar Afghanistan wato Burhan Qurbani ya shirya. Fim ɗin dai ya ƙunshi wasu musulmai matasa su uku dake zaune a birnin Berlin waɗanda suka samu kansu cikin hali ƙaƙanikayi dangane da imani da kuma al´adunsu.