Syria ta yi watsi da kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya | Labarai | DW | 01.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Syria ta yi watsi da kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Syria ta yi watsi da zargin da kwamitin sulhu na MDD ya yi mata cewa ba ta ba da cikakken hadin kai ba a binciken kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri. A lokacin da yake mayar da martani kan kuduri cikin fushi ministan harkokin wajen Syria Faruq al-Shara ya zargi kwamitin sulhu da dorawa kasarsa laifin kisan Hariri bisa zato. A jiya kwamitin sulhu na MDD yayi kira ga Syria da ta ba da cikakken hadin kai ba tare da gindaya wasu sharudda ba a binciken da ake yi na kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri. A cikin wani kuduri da aka amince da shi baki daya, membobi 15 na kwamitin sulhu sun yi barazanar daukar wasu matakai kan Syria idan ba ta yi biyayya da kudurin ba.. Rahoton binciken wannan kisa da mai shigar da kara na Jamus wato Detlev Mehlis ya gabatar, ya zargi manyan jami´an leken asiri Syria da na Lebanon da shirya harin bam din da ya halaka Hariri da wasu mutane 20 a cikin watan fabrairu da ya wuce.