Syria ta gayyaci komitin bincike na Majajalisar Dinkin Dunia a Damaskus | Labarai | DW | 09.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Syria ta gayyaci komitin bincike na Majajalisar Dinkin Dunia a Damaskus

Hukumomin Syria sun gayyaci komitin majalisar Dinkin Dunia mai bincike a kan mutuwar tsofan Praministan Labanon Raffik hariri, da su je birnin Damaskus, domin tantana batun hadin kan kasar, ga wannan bincike.

Hukumomin ,sun girka wani komiti na mussaman, wanda su ka azawa yaunin gudanar da bincike na daban ,a game da wannan kissa.

Rahoto binciken Komitin Majalisar Dinkin Dunia, ya zargi Syria da hannu dumu dumu a ciki kissan.

Sakataran kungiyar hadin kan Larabawa Amr Musa, ya tabbatar da cewa Syria, a shire ta ke, ta bada hadin kai.

Amr Musa, ya yi wannan kalamomi, jim kadan bayan wata ganawa da yayi, da shugaban kasar Syria, Bashar Al Assad.

Gobe ne ma, idan Allah ya kai mu, shugaban na Syria, zai gabatar da wani mahimmin jawabi a game da wannan batu.

A nasa bangare, sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia,Koffi Annan , ya kai ziyara aiki, yau a kasar Saudiyya, inda ya tantana, da hukumomin kasar a kan batun samun hadin kan Syria, domin gano haske a cikin bincike.