Syria ta buƙaci sojojin ta su kasance cikin shiri | Labarai | DW | 01.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Syria ta buƙaci sojojin ta su kasance cikin shiri

Shugaban ƙasar Syria Bashar al-Assad ya umarci dakarun sojin ƙasar su kasance cikin shirin ko ta kwana, a yayin da rikicin yankin gabas ta tsakiya ke ƙara yin ƙamari. Da sanyi safiyar Talata jiragen yakin Israila suka ragargaza hanyar da ta haɗe Syria da arewa maso gabashin Lebanon. Ministan harkokin wajen Syria Walid Muallem yace bai fidda tsammanin cewa Israila zata kaiwa ƙasar sa hari ba, a saboda haka yace wajibi ne su kasance cikin shiri na maƙarƙashiyar da Israila ke shiryawa da Amurka. A waje guda kuma Ministar harkokin wajen Syria Bouthaina Shaaban ta musanta zargin da Amurka ta yi cewa a yanzu Syria ta kasance saniyar ware a duniya.