Syria da MDD akan kafa kotun bincike | Labarai | DW | 27.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Syria da MDD akan kafa kotun bincike

Hukumomin Syria sun koka dangane da rashin tuntubarsu da akayi,akan batun kafa kotu ta musamman da zata binciki wadanda ake zaergi da hannu a jerin kashe kashe dake da alaka da siyasa a kasar Lebanon.A wata wasika daya aka aikewa sakatare general na mdd Kofi Anan,Jakadamn Syria a mdd Bashar Jaafari yace kafa wannan kotu ta musamman ba tare da shawarar Syria ba ,zai nunar dacewa Damascus bata da alaka da kotun.Wannan kotun mdd nada nufin binciken kashe kashen siyasa daya gudana a Lebanon,da kuma kisan gilla da akayiwa tsohon Premien Syria Rafik al-Hariri.