1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Syria da Iraq sun amince maida hulda bayan shekaru 25

November 21, 2006
https://p.dw.com/p/Buax

Kasashen Iraq da Syria sun amince da maida huldar diplomasiya tsakaninsu bayan katsewarta shekaru 25 da suka shige.

Ministan harkokin wajen Iraqi Hoshiyar Zebari ya sanarda haka wajen taron manema labarai na hadin gwiwa da takawaransa da Syria Walid Muallem,wanda ke kan ziyara a Bagadaza.

Jamian biyu sun kuma amince da hadin kai a fannin harkokin tsaro tsakanin kasashensu.

A shekarar 1982 ne dai aka yanke dangantaka tsakanin Iraq da Syria a lokacin mulkin saddam hussein.

A halin da ake ciki kuma ana sa ran shugaban kasar Iraqin Jalal Talabani zai kai ziyara birnin Teharan na kasar Iran a karshen wannan mako don tattaunawa da shugaban Iran Mahmud Ahmedinajad.