1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Switzerland ta yi watsi da shirin rabon kudi

Gazali Abdou TasawaJune 5, 2016

Al'ummar kasar Switzerland ta yi watsi da wani shiri na gwamnati da ya tanadi raba kudade kyauta ga duk dan kasar a karshen kowani wata, a zaben raba gardama da kasar ta shirya a wannan Lahadi.

https://p.dw.com/p/1J0vN
Schweiz Referendum Durchführungsinitiative
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Ehrenzeller

Kimanin kashi 78% ne 'yan kasar ta Switzerland suka yi watsi da wannan shiri wanda ya tanadi bai wa kowani dan kasa dama bakon da ya shekara biyar a kasar, kyautar kudi tsaba har Euro 2.260 a kowani wata, ko mutum yana da aikin yi ko kuma babu, da kuma Euro 600 ga kowani karamin yaro a kasar.

Akasarin al'ummar kasar ta Switzerland tana nuna adawa da wannan mataki na raba kudaden kyauta ga jama'a a bisa hujjar cewa hakan na iya karya darajar aikin yi a kasar.

Ko a shekara ta 2012 al'ummar kasar ta Switzerland ta yi watsi da wani shiri da ya tanadi tsawaita hutun mai albashi daga makonni hudu zuwa shida suna masu cewa matakin na iya rage kimar da kasar take da ita a idon kasashen duniya.